IQNA

Karba Kiran Manzon Allah (SAW) Shi Ne Tushen Hadin Kai Da Kauna

13:57 - December 27, 2015
Lambar Labari: 3470011
Bangaren siyasa, Dr Rouhani ya bayyana a lokacin bude taron makon hadin kai na kasa da kasa a karo na 29 cewa; dole ne mu yi koyi da abin da manzon Allah (SAW) ya koyar da mu domin samun hadin kai a cikin al’ummar musulmi.


Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, Hojj. Dr Hassan Hassan Rouhani shugaban kasar Iran ya fadi yau a lokacin bude taron kasa da kasa kan makon hadin kan al’ummar musulmi cewa, ya zama wajibi a kan dukkanin mabiya addinin muslunci da su yi aiki da koyarwa ma’aiki (SAW) a cikin lamurran rayuwarsu.

Ya ci gaba da cewa sakon da manzon Allah (SAW) ya zo ma duniya da shi ya kunshi dukkanin abin da dan adama yake bukata na tsarin rayuwarsa ta duniya baki daya, domin sako ne wanda ke shiryar da mutm zuwa ga dukkanin kyakkyawa tare da nisantar da shi daga duk wani mummuna.

Dr. Rouhani ya kara da cewa a halin da duniyar musulmi take rayuwa  ahalin yanzu, makiya sun gano barakar rashin hadin kai da ke tsakanin mabiya addinin muslunci kuma suna yin amfani da wannan damar wajen kara barakar da kuma cutar da musulmi a koina  acikin fadin duniya.

Dangane da abin yahudawan sahyuniya suke iaktawa kan al’ummar musulmin Palastinu kuwa, ya bayyana cewa hakan yana daga cikin abin da yake nuna rashin hadin kan musulmi, domin kwa da musulmi suna da hadin kai da hakan ba ta faru ba.

Wannan batu na mamayar kasar musulmi da yahdawan sahyniya suke yi, da kuma keta alfarmar wurare masu tsarki, ya kara tabbatar da wajabcin samun hadin kai a tsakanin dukkanin al’ummar musulmi matukar dai suna bukatar su rayu a cikin yanci, idan kuma ba haka ba to abin da yake faruwa  akan al’ummar palastinu yana nan zuwa a kan kowa daga cikin musulmi.

Tarihin rayuwar manzon Allah (SAW) yana koyar da mu hanyoyin warware lamurra da dama da suka zame mana karfen kafa, a tsakaninmu yana bukatar hakuri da yin aiki da hankali domin warware matsaloli, abin da ya shafi wajenmu kuwa, yana bukatar hadin kai da hada kalma guda wajen tunkarar kalu bale.

Dangane da yadda aka wayi gari kuma wasu suna yin amfani da sunan addinin muslunci wajen aikata ta’addanci kwa, shugaban kasa ya bayyan acewa muslunci ba ta’addanci ba ne, kuma bai koyar da dana dam ta’addanci ba.

Dr Rouhani y ace a kowane lokaci muslunci addinin zaman lafiya ne da fahimtar juna  atsakaninsa da sauran addinai, hatta ma yakunan da aka yi a cikin addinin muslunci a lokacin ma’aiki (SAW) an yi su ne a matsayin kare kai.

Ya kara da cewa babu wani lokaci da musulunci ya zama shi nre m,ai yin shishigi a kan sauran al’ummomi da addinai, idan kuma har wani ya yi haka saboda yana da mulki a hannunsa, to da sunan muslunci ya yi ba, kuma  alokacin bay a wakiltar muslunci ko ta vwace fuska.

Dr. Rouhani y ace idan muna sopn mu karba kiran manzon Allah (SAW) ta hanyar da ta dace, sai malamai daga cikinmu sun mike kai tsaye wajen ganin an samu hadin kai a tsakanin dukaknin al’ummar musulmi a duniya baki daya.

Daga karshe kuma ya bayyana yunkurin Imam Khomeni ® na kafa wannan mako na hadin kai a lokacin makon haihuwar manzon Allah (SAW) da cewa lamari da ke tattare da hikima, domin kuwa wannan mako shi ne makon da ya hada al’ummar musulmi baki daya.

3469778

Abubuwan Da Ya Shafa: iran
captcha