IQNA

Daya daga Cikin Masu Wakokin Bege A Masar Ya Rasu

16:30 - January 06, 2016
Lambar Labari: 3480029
Bangaren kasa da kasa, Sheikh Said Hafez daya daga cikin fitattun masu bege a gidajen takabijin da radio na kasar masar ya rasu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto dag shafin sadarwa na aynar gizo na Al-yaum Sabi cewa, Sheikh Said Hafez daya daga cikin fitattun masu bege Masar bayan fama da rashin lafiya a jiya ya rasu.

Babban hadakar masu gudanar da wakokin bege da yabo ga ma’aiki na kasar karkashin jagorancin Sheikh Mahmud Tuhami ne ya sanar da hakan a jiya.

A cikin bayabin sanarwar ya zo cewa gamayyar kungiyoyin masu bege na Masar za su gudanar da tarukan addu’a amasallacin Sayyidah Nafisa domin yin addu’a ga sheikh Said hafez.

Kafin wannan lokacin dai an ajiye a kan cewa sheikh said Hafez zai halarci wani taro na maulidin manzon Allah (SAW) a kasar Morocco, amma saboda tsanannin rashin lafiya bai samu damar tafiya ba.

Abin tuni a nan dais hi ne Sheikh Said Ismail an haife shi ne a garin Kassasin na lardin Isma’iliyya a cikin shekara ta 1951.

http://iqna.ir/fa/news/3464712


Ya yi karatun kur’ani mai tsarki a hannun sheikh Muhamamd Reshwan, haka nan kuma ya tashi a gidan malman addini, inda ya koyi wakokin yabo ga ma’aiki.

captcha