IQNA

Saudiyyah Ta Rusa Masallatai A Kasar Yemen

23:42 - January 22, 2016
Lambar Labari: 3480066
Bangaren kasa da kasa, Saudiyya da masu mara mata baya sun rusa masallatai masu tarin yawa a harin da suke kaiwa a kasar Yemen.
Saudiyyah Ta Rusa Masallatai A Kasar Yemen
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin tashar Alalam cewa, ofishin babban dakaraktan ma’aikatar kula da harkokin addinin A San’a y ace Saudiyya ta rusa masallatai 136 a cikin wannan lardi.

Kamfanin dillancin labaran Saba ya ce, ya nakalto daga Aiman Abdulkadir babban darakatan ma’aikatar kula da harkokin addini cewa, Saudiyya ta rusa masallati 49 kai tsaye a cikin birnin, wasu 87 kuma a wasu sassa na lardin.

Abdulkadir ya ci gaba da cewa yanzu haka akwai masallatai 19 da ta rusa a yankin Sanhan da Bani Bahlul, sai kuma wasu 13 a garin Hada da kuma 5 a Bilad Rus, 3 a Bani Matr, 3 kuma a Niham, sai kuma 4 a Hilam da khema Dakhilyah, da kuma Bani Hashish da Hujanah.

Ya kara da cewa kashi 80% na dukaknin masallatan da Saudiyya ta rusa a kasar Yemen suna da alaka ne da tarihi, wati masallatai ne wadanda aka gina daruruwan shekaru da suka gabata da ake lissafa su a cikin wuraren tarihi na kasar.

Abdulkadir y ace Saudiyya tare da kawayenta da suka hada da larabawa da turawa, su ne suke da hannu kai tsayea  dukkanin abin da yake faruwa na kisan fararen hula da rusa kasar Yemen.

3469260

captcha