IQNA

Ina 'Yan Ta'addan Daesh Suka Dosa Ne?

23:39 - January 23, 2016
Lambar Labari: 3480071
Bangaren kasa da kasa, daruruwan 'yan ta'addan Daesh suna ta tserewa daga kasashen Iraki da Syria suna tafiya zuwa kasar Libya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Trumpet cewa, saboda rashin zaman lafiya da sabain cikin gida a Libya, yan ta'addan Daesh sun mayar da kasar makomarsu.

Rahoton ya ci gaba da cewa tun a cikin shekara ta 2011 da gwamnatin marigayi Ghaddafi ta fadi, dubban yan ta'adda suka mayar da kasar Libya wata babbar madaddalrsu, inda suke ci gaba da isa can domin kafa babbar tungarsu.

Kimanin yan ta'addan daesh 500 ne aka tababtar da sun kama hanya zuwa kasar Libya domin hadewa da danginsu daga kasar Syria, alokacin baya adadin yan ta'addan a Libya ya kai 3000, yayin da kuma yanzu ya ninka har kimanin 10000.

A cikin shekara ta 2015 yan ta'addan kasar Libya sun fito daga kungiyoyi irin su Ansaru shari'a, da kuma wasu gungun nasu da ke Ajdabiya da sauransu, kuma su ne suka ci gaba da bunkasa suna mamaye wurare.

A halin yanzu dai mahukuntan kasar ta Libya sun kungiyar Daesh ta samu shiga cikin kasar kuma ta kafa ikonta awasu yankuna da ta kwace iko da su a gabashin kasar, musamman wadanna da ke arzikin man fetur.

'Yan ta'addan daseh sun yi amfani da man fetur da suke sacewa daga kasashen Syria da Iraki inda suke sayar da shi ga wasu daga cikin kasashen da ke makwaftaka da wadannan kasashe, kamar yadda kuma suke hankoron ganin sun mayar da Libya a haka.

3469535
captcha