
Kamfanin dillancin labaran iqna ya
habarta cewa ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo cewam kungiyar ta
PEGIDA za ta jagoranci gudanar da zanga-zanga a kasashe 14 na turai a cikin
mako mai zuwa, domin nuna rashin amincewa da a bin da suke kira musuluntar da
nahiyar turai, kasashen sun hada Chek, Jamus, Istuania, Solvakia da
Switzerland.
Daya daga cikin wadanda suka shirya
wannan taro ya bayyana cewa za su gudanar da nasua babban birnin kasar Chek, inda za su taru
domin nuna rashin yardarsu da kokarin mayar da nahiyar turai ta musulmi.
Ya ce dukkanin mutanen nahiyar turai
manufarsu guda ce ta rashin amincewa da musuluntar da wannan nahiya ta su.
Kungiyar PEGIDA dai an kafa ne a
cikin shekara ta 2014 a kasar Jamus, domin nuna rashin amincewa da yaduwar
addinin muslunci a kasar ta Jamus, daga bisani kuma akidar kungiyar ta ci gaba
da bazuwa zuwa wasu kasashen nahiyar turai.
Dangane da batun karbar yan gudun
hijira da gwamnatin Jamus ta ce ta yi da suka hada mafi yawansu musulmi,
kungiyar ta kara tsananata ayyukan na kiyaye da addini muslunci, kamar yadda ta
yi taro a kan hakan a birnin Colen na kasar Jamus.