Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Tanja24 cewa, a cikin watanni biyu masu zuwa ne za agudanar da wannan babban taro na duniya tare da halartar manyan malamai da masna daga ciki da wajen kasar.
Wannan dai shi ne karo na shida da za a gudanar da irin wannan taro, bayan gudanar da shi sau biyar a cikin shekaru biyar da suka gabata, inda a kan bahasi kan muhimman lamurra da suka shafi mujizar kur’ani mai tsarki.
Bisa ga alada dai akan bayar da dama ga mamalai da su gabatar da jawabai da kuma gabatar da makalolin da suka rubuta kan maudu’ai daban-daban da suka shafi mujizar kur’ani, wanda hakan yake a matsayin wani tarin karawa juna sani.
Malami d masana daga suka fito daga kasashen duniya suna yin iyakacin korinsu domin ganin sun baiwa traon hakkinsa, domin kuwa ko ba komai malakalolinsu da kuma jawabansu suna matsayin wani abu da ke wakilatra sauran muslmi da ba su samu halartar taron ba.
Dag akarshe akan gayyaci wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin kasar da ska hada da ministan harkokin addini da na ilimi domin rufe taron, da kuma yin godiya da dimbin bakin da suka halarta daga kasashen duniya.