IQNA

23:52 - March 25, 2016
Lambar Labari: 3480261
Bangaren kasa da kasa, babban masallacin birnin Brussels na kasar Belgium ya yi Allawada da kakakusar murya dangane da harin ta’addancin da aka kai a birnin.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Euro News cewa, musulmi mambobin kwamitin babban masallacin Brussels sun yi Allawadai da harin ta’addanci da aka kai a birnin.

Biyu daga cikin mambobin kwamitin masallacin sun zanta da manema labarai, inda suka bayyana musu cewa abin da faru abin Allawadai ne, kuma ba shi da alaka da musulmi.

Suka kara da cewa wadanda suka kai wannan harin ba musulmi ba ne, ko da kuwa sun kira kansu musulmi, domin kuwa muslunci addinin zaman lafiya da fahimtar juna ne.

Muhammad Glay babban limamin masallacin ya bayyana cewa, tun ranar da aka kai harin ya fitar da bayani, wanda ya bayyana matsayin musulmin birnin dangane da wanann hari na ta’addanci, inda ya ce bas u da alaka da harin.

Ya kara da cewa ba wai kawai ba su da alaka da harin ba ko wadanda suka kais hi, suna ma nema da dauki matakan dasuka dace domin gano duk wanda yake da hannuna cikinsa domin hukunta shi, domin yan ta’adda bas u wakiltar musulunci.

Harin ranar talata da ta gabata dai yay i sanadiyyar mutuwar mutane tare da jikkatar wasu a lokacin da yan ta’addan suka tayar da bam a cikin filin jirgin sama da tashar jirgin kasa.

Yanzu haka dai ana ci gaba da neman wadanda suke da alaka da wanna hari kowane sako na birnin, bayan kasha wadanda suka kais hi kai tsaye.

3484487

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: