IQNA

Kur'ani Da Aka Danganta Da Iamm Ali (AS)

20:29 - April 19, 2016
Lambar Labari: 3480337
Bangaren kasa da kasa, cibiyar kula da hubbaren Imam Ali (AS) ta kafa wani kwamiti domin gudanar da bincke kan wani kur'ani da aka danganta da shi.
Kamfanin dillancin labaran iqn aya ahbarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na hubbaren Hussaini cewa, Isa Muhammad saleh Alkhersan shugaban kwamitin shawara na hubbaren Alawi ya bayyana cewa, domin buga kwafin kur'anin da ak edangatawa da Imam Ali (AS) ana gudanar da bicike na hakika.

Wannan kwamiti da aka kafa domin gudanar da biciken da ya kamata karkashin sayyid Nazzar Hashem Hablul Matin, zai fara gudanar da ayyukansa nan ba da jimawa ba.

Kamar yadda kuma wannan kwamiti zai kunshi mambobi na masana kan harkokin rubutu da kuma tarihin rubutun gami da masana ilimin kimiyyar gane daddun abubuwa na tarihi, kamar yadda kuma wasu daga cikin malaman jami'oi za su shigo cikin lamarin.

Daga cikin abubuwan da za a gudanar har da daukar samfuri na kwayoyin hallita na takardun da aka yi rubutun a kansu, da kuma nauyin tawadar, gami da yadda aka yi rubutun da salonsa, domin gano lokaci da aka yi shi, da kuma sanin dangantakarsa da Imam Ali (AS)

Alkhersan ya ce ya zuwa yanzu an kammala dukaknin shirin da ya kamata domin fara gudanar da wanann gagarumin aiki, wanda yake da bababr kima ta fuskar tarihi ga dukkanin musulmi, da kuma cibiyoyin binciken ababen tarihi na kasa da kasa.

3490081

captcha