
Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gioz na (GToday) cewa, ita wannan gasa za ta gudna ne ta hanyoyi na sadarwa, kuma kamfanin Khallaq na tattalace-tallace ne zai uki auyin gasar tare da bayar da kyautuka masu tsoka.
Gasar dai za ta fi mayar da hankali ne a cikin yankin gabas ta tsakiya, da kuma kasashen arewacin nahiyar Afirka, inda za a rika duba abubuwan da aka saka da suke da alaka da watan Ramadan mai alfarma.
Daya daga cikin masu shirya gasar ya bayyana cewa, babban muhimmancin wannan gasa shi ne, kara karfafa gwiwar musulmi da larabawa wajen bayar da muhimmanci ga lamarin da ya shafi watan azumin Ramadan mai alfarama.
Bisa ga al’ada dai kasashen larabawa da na musulmi suna bada muhimamnci matuka a cikin watan Ramadan ga lamurra da suka shafi azumi da kuma kokarin taimaka ma masu rauni, da kushirya abubuwa na farin ciki da yada rahama a koina da tausayia cikin al’umma, domin samun albarkacin wanann wata.