
Kamfanin dillanicn labaran iqn aya habartacewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na yaum Sabi cewa, Abdulrahman Allawi, babban daraktan cibiyar kula da ayyukan masallatai a kasar ya bayyan acewa za s gudanar da taronsu a daren yau.
Ya ce wasu daga cikin malamai da kuma jami’an gwmnati za su halarci wannan taro a wannan dare mai albarka.
Allawi ya kara da cewa a wannan taro Sheikh Zainul Abidin Abdullatif da kuma Ali Taifur babban mai bayar da shawara kan harkokin addini na lardin, da kuma Muhammad Abdulaziz wakilan jami’ar Azahar dk za su halarci wannan zaman taro.
Daren sha biyar ga Sha’aban ba wai kawai ga mabiya mazhabar shi’a ne yake da muhimmanci ba, yana da muhimamnci ga wasu daga cikin yan snna, wadanda suka yi imanin cewa acikin wannan daren ne ake rarraba komai da ya shafi bayi a cikin shekara.
A saboda haka suke gudanar da ayykan ibada da ya hada da sallol da istigfari da kuma sauran ayyukan ibada.
Ya zo a cikin wasu ruwayoyi cewa a wannan daren ne Allah ya karbi addu’ar manzonsa (SAW) ta nemkan a canja masa alkibla daga masallacin Qsa zuwa ka’abah.
Daren sha biyar ga sha’abandai shi ne daren haihuwar Imam Zaman (AJ) wanda ake raya shi da addu’oi da ibada da kuma taruka na tunawa da imamin tsira na goma sha biyu.