IQNA

Haramtacciyar Kasar Isra'ila Ta Kayyade Adadin Palastinawa Masu salla A Quds

23:58 - June 17, 2016
Lambar Labari: 3480524
Bnagaren kasa da kasa, haramtacciyar kasar Isra'ila ta dauki matakan hana palastinawa gudanar da salla a cikin masallacin Aqsa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo nan a palastinu cewa, gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta dauki matakan hana palastinawa gudanar da salla a cikin masallacin Aqsa a cikin wannan wata mai alfarma.

Bayanin y ace gwamnatin yahudawan ta kayyade adadin da cewa kada ya wuce mutane dubu 200 baki daya, a daidai lokacin da ake samun mutane kusan rabin muliyan da suka halartar sallar Juma'a a cikin Ramadan a masallacin mai alfarma.

Kafin wannan loacin gwamnatin yahudawa tana hana palastinawa da shekarunsu ke kasa da hamsin yin salla a cikin masallacin, amma saboda kusantuwar lokacin gudanar da ranar Quds ta duniya ta wannan sabon matakin.

Bisa ga al'ada dai palastinawa sukan cika masallacin da kewayensa domin raya ranar quds ta duniya a karshen kowane wat ana Ramadan mai alfarma.

captcha