IQNA

An Gudanar Da Gasar Hardar Kur’ani Mai Tsarki A Afirka Ta Kudu

23:36 - June 26, 2016
Lambar Labari: 3480555
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da gasar hardar kur’ani mai tsarki ta kasa baki a kasar Afirka ta kudu.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizona hqmi.org cewa, an gudanar da wannan gasa ne karkashin shirin cibiyar kula da ayyukan mulsunci ta birnin Capetown.

Bayanin ya ce an samu halartar mahardata daga sassa na kasar, gami da kuma alkalai guda 6 a karkashin jagorancin Sheikh Abdullah Awaliddin, shugaban cibiyar kula da harkokin mulsunci ta birnin.

A yayin kamala taron gasar, an bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka nuna kwazo, kamar kuma yadda aka bayar da kyautka na baki, wanda baban limamin birn Sheikh Muhammad Ihsan ya jaggoranci mikawa, kamar yadda kuma sheikh Riyadh Iftar da kuma Sheikh Ahmad Abdulrahman Alakish suka taya shi mika kyautukan.

Kafin kamala taron rufe gasar, an gabtar da jawabai, inda aka ja hankalin matasa musulmi musamman, da su mayar da hankali matuka ga lamarin kur’ani mai tsarki, tare da koyon hukuncin karatunsa wati tajwidi, gami da bayar da himma wajen misiltuwa da koyarwarsa a cikin lamurran da suka danganci rayuwa.

3510495

captcha