Kamfanin dillanicn labaran iqna
ya habarta cewa ya nakalto daga Jaridar Quds Al-arabi mallakin gwamnatin
atar da ake bugawa abirnin landa ta bayar da rahoton cewa, mahukuntan kasar ta
Bangaladesh sun ce Zakir Naik wanda malamin salafiyyah ne, yana yada tsatsauran
ra'ayi, kuma dukkanin matasa biyar da suka kaddamar da harin ta'addanci tare da
kashe mutane 22 a makon da ya gabata, sun tasirantu ne da kalamansa da ake
watsawa ta hanyar wannan tasha, a kan haka an rufe tashar tare da haramta masa
shiga kasar.
Assad Zaman Khan ministan harkokin cikin gidan kasar Bangaladesh ya fadi jiya a zantawarsa da manema labarai cewa, jami'an tsaron kasar suna cikakken bayanan sirri kan cewa dukkanin masu alaka da kungiyoyin 'yan ta'adda a kasar mutanensa ne, kuma yanzu suna bincike kan kasashen da suke daukar nauyinsa da ba shi kudade wajen yada akidar salafiyanci da wahabiyanci da ke haifar da tsatsauran ra'ayi wanda ke kai matasa shiga kungiyoyin 'yan ta'adda.
Wasu daga cikin kasashen turai da Asia sun kafa dokar hana Zakir Naik shiga cikin kasashensu, bisa abi da suka kira kauce wa yada tsatsauran ra'ayi a tsakanin matasa musulmi.