
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na New Times cewa, kimanin matasa 60 daga kasashe 9 na Afrika da ke halartar gasar karatun kur’ani a birnin Kigali na kasar Rwanda sun nuna rashin jin dadi dangane da kisan kiyashin da aka yi a kasar a shekarun baya.
Masu halaratr gasar sun ziyarci wurare na tnawa da kisan kiyashin da aka yi a kasar a cikin shekara ta 1994, inda kimanin mutane dubu 250 suka rasa rayukansu.
Cikin shekara ta 1994 jirgin da ke dauke da shugaban kasar Journa Habiarimana ya fadi a kusa da birnin Kigali babban fadar mulkin kasar, wannan ya sanya yan kabilar Hutu suka zargi yan kabilar Tutsi da hannu wajen kifar da jirgin, wanda hakan ya jawo tashin hankali a lokacin da Hutu suka yi ta kasha Tutsi da sunan daukar fansa.
Ahmad Sidqi daya ne daga cikin masu halartar wannan gasar kur’ani ya bayyana cewa, hakika abin da ya faru a wannan kasa babban abin bakin cikine da takaici, domin kuwa hakan ya nuna rashin sanin kimar dan adam da wasu suka nuna.
Ya kara da cewa ya kamata a bin da ya faru a kasar Rwanda a cikin wancan lokaci ya zama babban darasi ga dukkanin al’ummomin Afirka, da su hada kansu su zauna lafiya da juna.
Kamar yadda kuma sauran masu halartar gasar suka yi fatan kasar Rwanda ta ci gaba da kara samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, musamman ma a wannan lokaci da kasar take samun ci gaba fiye da kowane lokaci a tarihinta.