IQNA

Shekhul Azhar: Dole Ne Malamai Su Haramta Rikicin Sunnah Da Shi’a

23:42 - July 25, 2016
Lambar Labari: 3480645
Bangaren kasa da kasa, Ahmad Tayyib babban malamin cibiyar Azahar ya bukaci malamai na dukkanin bangarorin sunnah da shi’a da su fitar da fatawa ta haramta rikici a tsakanin bangarorin biyu.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Alalam cewa, Ahmad Tayyib a lokacin da yake amsa tambayoyin maneama labarai ya bayyana cewa, babu wani dalilin da zai sanya bangarorin musulmi na shi’a da sunnah su yi rikici da juna, domin kuwa dukkanin musulmi a hukunci na muslunci domin dukkaninsu sun sheda kalmomi biyu na shahada.

Ya ce cibiyar Azhar za ta ci gaba da yin kokari domin ganin an samu daidaiton fahimta a kan kana binya hada musulmi shi’a da sunna, sauran abubuwan da ake da sabani a kansu na fikihu da sauran batutuwa na ilimi, wannan lamari ne da ya shafi malamai, kuma za a iya samun mafita ta yadda kowa zai rike fahimtarsa da aka sammu sabani a kanta, amma a yi aiki tare a kana bin da ya hada dukakknin bangarorin musulmi.

Shehin malmin ya ce yanzu haka ya umarci manyan malaman cibiyar Azahar da su zauna su fitar da fatawa ta haramta rikici ko kafirta juna tsakanin ‘yan sunnah da ‘yan shi’a, domin kuwa an yi manyan malamai a wanann cibiya ta Azahar na shi’a da sunna fiye da shekaru dubu da suka gabata, amma Azahar ba ta san da wani rikci makamancin haka ba sai a wannan zamani.

Malamin ya ce akwai wasu ‘yan tsiraru a cikin dukkanin bangarorin da suke ruruta wannan wutar rikici da fitina, wanda nauyi ne da ya rataya kan manyan malamai na sunnah da shi’a su kawo karshen haka, ta hanyar fitar da fatawoyi na wajabcuin hadin kai da nisantar rikici da kafirta juna.

3517516

captcha