Bayanin ya ce masarautar Bahrain tana tafka babban kure, domin kuwa malaman da take kamawa su ne suke tausasa al'ummar kasar daga yin duk wani gagarumin bore da zai kifar da masarautar baki daya, kuma ci gaba da yin hakan zai gaggauta kawo karshen mulkin masarautar kama karya da turawan mulkin mallaka suka kafa a kasar.
A baya-bayan nan masarautar Bahrain ta kame manyan malamai da suka nuna rashin amincewarsu da matakin da ta dauka na janye izinin zam dan kasa daga kan babban malamin addini na kasar Sheikh Isa Kasim, malamin da fiye da rabin al'ummar kasar ke kallonsa a matsayin shugabansu an addini.
Daga cikin manyan malaman da aka kame a cikin makon nan har da Sayyid majid Mash'al, shugaban majalisar malaman kasar, da kuam sheikh Ali Muhli, da sheikh Fadil Zaki, da kuam Sayyid Muhsin Al-guraifi, dan Allamah Al-guraifi.