IQNA

Samar Da Littafan Koyar Da Kur'ani A Algeria

23:58 - August 09, 2016
Lambar Labari: 3480694
Bangaren kasa da kasa, an samar da wasu sabbin littafai na koyar da kur'ani a makarantun kasar Algeria.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na Iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gizo na Alshuruq cewa, mahukunta a kasar Algeria sun samar da wani tsari raba littafai sabbi na koyar da daliban kur'ania makarantu.

Bayanin y ace wannan tsari ya kunshi raba littafan ne ga makarantu na gargajiya da ake koyar da kur'ani ta tsohuwar hanya, wadanda suke yin rubutu kan allo na katako, inda yanzu za su rika yin amfani da wasu littafai.

Wannan tsari bay a kore yin amfani da alluna ba ne, zai taimaka ma daliban ne wajen yin sauri da kuma kammala karatunsu cikin lokaci ba tare da jimawa kamar tsohon tsari ba.

Kasar Algeria dai na daga cikin kasashen arewacin nahiyar Afirka da ke Amani da tsarin karatun allo kamar sauran kasashen yammacin nahiyar, wanda hakan kuma yana asali da tarihi a kasar.

Yanzu haka dai an far araba litafan ga makarantun, kuma an fara yin amfani da su, kuma dalibai da malamai sun gamsu da yadda aka tsara littafan da kuma salonsu na koyar da kur'ani.

3521455

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna littafan taimaka tsari algeria
captcha