Kamfanin dillancin labaran kur’ani na Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar hafinton post cewa, wannan yar wasa ta dauki hankulan al’ummomin duniya, misamman ma kafofin yada labarai.
Ganin cewa wannan yar wasa tana sanye da hijabin mulsunci, amma hakan bai hana ta gudanar da abin da ta sanya a gaba ba, duk kuwa da cewa ba ta samu lambar zinari ba, amma tayi rawar gani kuma tra burge jama’a da dama.
Ibtihaj Muhammad ta bayyana a matsayin musulma kuma yar kasar farasana cikin gasar wasannin Olympics ta duniya, a daidai lokacin da dan takarar shugabancin kasar Amurka Donald Trump yake ta kara matsa kaimi wajen sukar musulmi da musulunci a idon duniya.
A lokacin da take amsa tambayoyin manema labarai ta mayar da martini dangane da furucin Donald Trump, inda take cewa; hakika abin da yake fada yana da matukar hadari.
Ta kara da cewa ita yar kasar Amurka ce kuma bakar fata, kuma ita musulma ce ga shi kasantuwarta musulma bai hana ta wakilatr kasar Amurka a wanan gasa ba, a kan haka ta ce nuna kyamar wani jinsin mutane saboda addini ko akida ya sanawa ‘yan adamtaka, har da dokokin kasar ta Amurka.
Ibtihaj Muhammad a zantawarta da tashar talabijin ta CNN ta bayyana cewa, a matsayinta na mace musulma bakar fata daga Amurka, hakan bai hana kiyaye dokar addininta ba, a kan haka wannan babban abin lura ne ga sauran mata musulmi, da kada su kasa a gwiwa wajen taka rawa a fagagen da suka kware amma tare da kiyaye kaidoji da kuma dokoki daidai da fahimta ko akida ta addini.
Wanann yar wasa ta samu nasara a kan abokoiyar karawarta daga kasar Ukraine, amma wata yar kasar Faransa ta yi nasara akanta, wanda hakan ya sa ba ta samu zinariya ba, amma dai tan da sauran wasa a gabanta a nan gaba.