Babban abin da shirin ke mayar da hankalia kansa dai shi ne hardar kur'ani mai tsarki wanda mata 83 ke halarta, da aka raba su zuwa rukuni 7, kuma kuyar da wasu muhimman ilmomi da suka shafi hukunce-hukuncen karatun kur'ani mai tsarki.
Haka nan kuma bayanin ya kara da cewa wannan shiri ya kebanci mata ne zalla, kama daga masu yawan shekaru da kuma yan mata wadanda suke da bukatar halartar shirin, wanda saboda masu zuwa makaranta ne da suke hutun bazara ake saka wannan ajujuwa.
Fatima Falasi ita ce babbar darakta ta cibiyar Al-nahdah, ta bayyana cewa suna gudanar da wanans hiri ne da nufin kara fada ayyukan kur'ani da kuma al'adun muslucni a tsakanin mata musulmi, ta yadda hakan zai bar kyakyawar tasiri a cikin zukatansu.
Ta kara da cewa baya ga koyar da hardar kur'ani mai tsarki, suna saka wasu ajujuwa na koyar da kyawawan dabiu na muslunci, da ma wasu hukunce-hukunce da suka shafi mata a muslunci, da yadda ya kamata su yi rayuwarsu bisa ilimin addini.