IQNA

Ma'aikatan Kamfanin Buga Kur'ani Sun Yi Yajin Aiki A Saudiyyah

23:51 - August 11, 2016
Lambar Labari: 3480700
Bangaren kasa da kasa, ma'aikatan kamfanin buga kur'ani na sarki fahad sun yi yajin aiki saboda rashin biyansu albashinsu kan lokaci.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Uyun Khalij cewa, daruruwan ma'aikatan kamfanin buga kur'ani na sarki fahad da ke birnin Madinah Munawwarah sun yi yajin aiki saboda jinkin biyansu albashinsu.

Bayanin ya ce tun kafin wannan loacin ma'aikatan sun sha kokawa kan matsalar rashin biyansu albashi akn lokaci, amma hakan bai yi wani amfani ba, saboda haka suka yanke shwar shiga yajin aiki somin nuna rashin amincewarsu da hakan.

Da dama daga cikinsu sun bayyana cewa rashin biyansu kudadensu kan kari ya jawo musu matsaloli da dama atsakaninsu da iyalansu, wadanda suke daukar nauyinsu da kudaden albashin da suke karba.

Yanzu haka dai mahukunta a kasar ta Saudiyyah suna yin dubi dangane da wannan matsala, duk kuwa da cewa ba su bayyana komaia a hukumance ba kan lamarin.

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna
captcha