IQNA

Jagoran Juyin Islama:

Ma’aikatar Tattara Bayanan Sirri Kashin Bayan Wanzuwar Tsarin Muslunci Ce

23:14 - August 12, 2016
Lambar Labari: 3480701
Bangaren kasa da kasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da minista, mataimakan minista da manyan daraktocin Ma'aikatar tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirri na kasar Iran inda ya bayyana ma'aikatar a matsayin wata cibiya mai matukar muhimmanci.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jagora cewa, A ranar Talata ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da minista, mataimakan minista da manyan daraktocin Ma'aikatar tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirri na kasar Iran inda ya bayyana ma'aikatar a matsayin wata cibiya mai matukar muhimmanci kana kuma idon tsarin Musulunci na kasar Iran, yana mai cewa: Ma'aikatar tsaron cikin gida dai wata garkuwa ce ga tsarin nan na Musulunci, wanda ta kowace fuska bai kamata a bari ta cutu ba.

Haka nan kuma yayin da yake mika godiyarsa dangane da irin hidima da kokari ba dare ba rana da bangarori daban-daban na ma'aikatar suke yi, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar nasara da kuma ci gaban juyin juya halin Musulunci sun ginu ne bisa tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali. Daga nan sai ya ce: Rashin nasarar da ma'abota girman kan duniya suka fuskanta a fadar da suke yi da gwamnatin Musulunci (ta Iran) duk kuwa da irin makirce-makircen da suka dinga kullawa tun ranar farko na nasarar juyin juya halin Musulunci, lamari ne da ba za a iya cimma shi ba in da ba don tsaron da ake da shi ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana duk wani kokari na raunana tsaron mutane da jami'an gwamnati a matsayin cin amana yana mai cewa: Karfi na kariya da ya kiyaye kasar nan tsawon wadannan shekarun, shi ne wannan karfi na tsaro. Don haka matukar aka raunana wannan karfin, to kuwa za a fuskanci matsaloli da bala'oi daban-daban.

A saboda haka ne Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada wajibcin karfafa bangaren imani da kusaci da Allah a Ma'aikatar tsaron cikin gidan inda ya ce: Ma'aikatar tsaron cikin gidan wata garkuwa ce na wannan tsari na Musulunci, wanda ta kowace fuska bai kamata a bari a cutar da ita ba. A saboda haka wajibi ne a ba da muhimmanci ga karfafa abubuwa masu muhimmanci irin su imani da kusaci da Allah a wannan ma'aikatar sama da sauran cibiyoyi na daban.

Haka nan yayin da yake ishara da irin karfi da kuma kwarewa ta matasa muminai masu riko da koyarwar juyin juya halin Musulunci da ake da su a Ma'aikatar tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirrin, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Ku yi kokari wajen karfafa koyarwa ta juyi a cikin ma'aikatar tsaron cikin gidan.

Ayatullah Khamenei ya bayyana Ma'aikatar tsaron cikin gidan a matsayin idon tsarin Musulunci, don haka sai ya ce: Wajibi ne a kiyaye koyarwa da mahangar juyin juya halin Musulunci a ma'aikatar tsaron cikin gidan.

Jagoran ya bayyana jawabai da kalaman marigayi Imam Khumaini (r.a) a matsayin koyarwa da kuma tushen juyin juya halin Musulunci, don haka sai ya ce: Shata kan iyaka da ma'abota girman kan duniya karkashin jagorancin Amurka na daga cikin tsuehn koyarwar marigayi Imam Khumaini (r.a), don haka babu wani sassauci da za a yi dangane da wannan lamarin.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Wajibi ne ma'aikatar tsaron cikin gida ta kasance mai jiran dakon makiya a duk wani wajen da suka dana tarkonsu da nufin cutar da gwamnatin Musulunci, sannan kuma su dauki hakan a matsayin fagen aikinsu.

Rawar da ma'aikatar tsaron cikin gidan za ta taka wajen tabbatar da siyasar tattalin arziki na dogaro da kai yana daga cikin bangarorin da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da su. Jagoran ya ce: Hanyar magance matsalolin da ake fuskanta a kasar nan ita ce riko da tattalin arziki na dogaro da kai, wanda tuni aka fara aiki a wannan bangaren. To amma wajibi ne a dinga ganin sakamakon wannan aikin a kas.

Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da irin rawar da ma'aikatar tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirri za ta taka wajen maganin masu ta'annuti ga tattalin arzikin kasa.

Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musuluncin, sai da ministan ma'aikatar tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirrin Hujjatul Islam wal muslimin Alawi ya gabatar da jawabinsa dangane da irin ayyukan da ma'aikatar ta yi da kuma abubuwan da ta sa a gaba.

3521564

captcha