Bayanin ya ce jiragen yakin na Saudiyya sun kai harin ne da gangan a kan makarantar ta kur'ani, inda mutane ashirin da hida suka yi shahada wasu da dama kuma suka samu raunuka, baynain ya ce daga cikin wadnda suka rasu shida mutanen gari ne, ashirin kuma daliban kur'ani ne.
Haka nan kuma bayanin ya kara da cewa tun bayan da masarautar iyalan gidan Al saud sun jima suna kai hari kan al'ummar Yemen yanzu haka majalisar dinkin duniya ta fitar da wani rahoto a jiya dangane da adadin mutanen da suka rasa rayukansu tun bayan da Saudiyyah ta fara kaddamar da hare-hare kan al'ummar kasar Yemen a cikin watan Maris na shekara ta dubu biyu da sha biyar.
Mai magana da yawun kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya Ravina Shamdasani ce ta sanar da rahoton a jiya wanda aka mika wa kwamitin tsaron Majalisar dinkin duniya.
A kwanakin baya ne babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban ya cire sunan Saudiyyah daga cikin rahoton da majalisar ta harhada kan kisan kanan yara kusan dari takwas da Saudiyya ta yi a cikin shekarar dubu biyu da biyar a Yemen, saboda abin da ya kira barazaar da aka yi a kansa, lamarin da ke ci gaba fuskantar kakkausar suka daga kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa.