Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin tashar alalam cewa, Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar kungiyar Hizbullah ta dakile da kuma hana "Isra'ila" cimma dukkanin manufofinta na kaddamar da yaki a kan kasar Labanon a shekara ta 2006, yana mai cewa "ana daukar wannan nasarar daga cikin lamurra masu muhimmanci da aka cimma a yayin yakin don kuwa ta dakile manufar da Amurka take son cimmawa ta hanyar yakin. Saboda an kaddamar da yakin ne bisa umurnin Amurka. Don haka babbar nasara ce kasar Labanon ta samu.
Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabin wajen bikin tunawa da shekaru 10 da wannan nasara da aka gudanar a garin Bint Jubeil da ke kudancin kasar ta Labanon inda ya ce: "Daga cikin muhimman abubuwan da aka cimma yayin yakin shi ne sakamakon yakin" don haka sai ya kirayi masana da kwararru da suke yi darasi da kuma dubi cikin sakamakon yaki a fagen soji, al'adu, tattalin arziki da zamantakewa da sauran don fahimtar wani bangare na nasarar da aka samu a yakin na shekara ta 2006".
Sayyid Nasrallah ya ce: "Daga cikin wadannan sakamako har da girgiza cibiyar sojin "Isra'ilan" daga cikinta ta yadda a halin yanzu cibiyar tana cikin mawuyacin yanayi na rauni kai da ma kusan rugujewa gaba daya. Sayyid ya ci gaba da cewa: "Sabanin da rarrabuwan kai da aka samu tsakanin jagororin sojin "Isra'ilan" a bangare guda, sannan a wani bangaren kuma tsakaninsu da sauran sojojin lamarin da ya kai kowa da zargin dan'uwansa da cin amana". Yana mai cewa ba a taba ganin irin wannan yanayi a tarihin haramtacciyar kasar Isra'ilan ba lamarin da ya haifar da rashin yarda a cikin cibiyar sojojin.
Sayyid Nasrallah yayi ishara da cewa: "Daga cikin sakamakon yakin shekara ta 2006 shi ne tabbatar da rashin yardar Isra'ilawa ga sojojin sahyoniyawan da cewa suna da karfin kawo karshen yaki da kuma samun nasara, wanda hakan shi ne mafi hatsarin lamarin a haramtacciyar kasar Isra'ilan". Sayyid ya ci gaba da cewa: "Kamar yadda kuma yakin ya sanya rashin yardar 'yan siyasa da sojojin "Isra'ilan". Sayyid Nasrallah ya ce: "Yardar da sojojin "Isra'ila" suke da ita ga jagororin siyasar ta girgiza ainun a yayin yakin 2006 kamar yadda yardar da al'umma suke da ita ga jagororin siyasar ita ma ta girgiza. Sayyid Nasrallah ya ce: Bayan shekaru 10 da yakin "Isra'ilan" ta gaza wajen sake dawo da karfinta na soji, ta yadda a halin yanzu ma an dawo da tambaya dangane da yiyuwar ci gaba da wanzuwar haramtacciyar kasar Isra'ilan.
A wani bangare na jawabin nasa Sayyid Nasrallah ya ce: "Isra'ilawa suna gaskata abubuwan da kungiyar gwagwarmaya (Hizbullah) ta fadi, don haka a halin yanzu muna sanar da su cewa babu wani waje a duk fadin haramtacciyar kasar Isra'ilan da makamanmu masu linzami ba za su iya kai wa wajen ba", yana mai cewa: "Bayan yakin shekara ta 2006 a halin yanzu "Isra'ila" ta gaza wajen sanar da manufarta a yayin yakin Gaza hakan kuwa saboda tsoron da suke da shi ne na gazawa wajen cimma su. Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: "Sakamakon yakin shekara ta 2006, firayi ministan haramtacciya kasar Isra'ilan Netanyahu yana cewa mun san cewa yaki mai zuwa idan har aka tilasta mana za ta kasance mai tsanani sosai, to amma duk da hakan dai za mu yi nasara don kuwa ba mu da wani zagaye na biyu". Don haka sai ya kirayi Netanyahun da cewa: "Ku din nan wata al'umma ce mai rauni wacce ta fi gidan gizo gizo rauni, al'ummar da ta gaji daga yaki da kare kanta", yana mai cewa nasarar yakin shekara ta 2006 ya cutar da "Isra'ila" daga tsakar zuciyarta ta yadda a halin yanzu "Isra'ilan" tana cikin tsoro da fargaba alhali a baya sabanin hakan lamarin yake.
A jawabin nasa, Sayyid Nasrallah ya lissafa wasu daga cikin manufofin da "Isra'ila" ta so cimmawa a yayin yakin wadanda ta gagara cimma su. Daga cikinsu akwai: Murkushe kungiyar Hizbullah wanda shi ne babban manufar yakin daga nan kuma da cimma mafi girman ruguzawa da kashe dakaru da jagororin kungiyar gwagwarmaya da lalata karfin da take da shi da kwance damararta da kawar da Hizbullah daga duk wani fage na siyasar Labanon da yankin nan. Sayyid ya ci gaba da cewa: "Daga cikin manufofin wannan yaki har da kwace makaman kungiyar gwagwarmaya daga kudancin yankin Litani da sanya yankin kudancin Litanin ya zamanto yankin da babu mutane".
Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: "Daga cikin wadannan manufofin da aka dakile su ita ce tilasta shigo da sojojin kasashen duniya daban-daban kamar wacce take mamaye da Iraki (a wancan lokacin) da baza wadannan sojoji a kan iyakokin kasashen Labanon da Siriya da nufin hana samar da sabuwar gwagwarmaya da sanya Labanon cikin siyasar Amurka da kawayenta a yankin da sake farfado da karfin "Isra'ila" wanda ya yi rauni sosai bayan shekara ta 2000 da kuma sake sojojin 'Isra'ila" guda biyu da ake rike da su. Sayyid ya ci gaba da cewa: "Mafi girman dukkanin wadannan shi ne abin da tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Condalizza Rice ta sanar na haihuwar sabuwar Gabas ta tsakiya daga nan kuma sai tabbatar da ikonsu a Siriya da kawar da kungiyoyin gwagwarmaya a Palastinu da killace Iran da mayar da ita saniyar ware, wanda hakan yana nufin tabbatar da ikon Amurka a dukkanin yankinmu na tsawon daruruwan shekaru". Yana mai jaddada cewar dukkanin wadannan manufofin sun sha kashi a yayin yakin shekara ta 2006 albarkacin sadaukarwar mujahidai da wadanda suka sami raunuk da fursunonin yaki da iyalai da sojojin Labanon da tsayin dakan al'umma da kungiyoyi haka nan da kuma sakamakon cikakken tsarin gudanarwa da hadin gwiwan da aka samu yayin yakin.
Yayin da ya koma kan abubuwan da ke gudana a yankin Gabas ta tsakiya kuwa, Sayyid Nasrallah ya bayyana cewar: "Hizbullah ita ce aka fi nufa a tsakankanin sansanin 'yan gwagwarmaya hakan kuwa shi ne yake fassara dalilin da ya sanya ake yakanta ta hanyar amfani da 'yan amshin shata 'yan ta'adda" yana mai cewa: "Amurka ita ce ta kirkiro kungiyoyi masu kafirta musulmi wadanda suka faro daga Al-Qaida zuwa Da'esh zuwa Nusra don haifar da irin wannan hargitshi da rashin tsaron da ke faruwa a yankin namu tana mai dogaro da siyasar yaki na wakilci ta hanyar taimako da goyon bayan kasar Saudiyya da sauransu da kuma ta hanyar saukaka musu hanya da bude musu kan iyakoki".
Sayyid ya ci gaba da cewa: "Da'esh da sauran kungiyoyin 'yan ta'adda sun zamanto wasu hanyoyi na yakin neman zabe Amurka da yake Amurkawan sun yi amfani da wadannan kungiyoyi na 'yan ta'adda, a yanzu kuma lokacin gamawa da su yayi don cimma wata manufar da ake da ita a hankalin yanzu. Wannan kuwa shi ne abin da a baya na taba fadi wa dukkanin kungiyoyin 'yan ta'addan".
Sayyid Nasrallah ya kirayi "Dukkanin kungiyoyin 'yan ta'adda da suke Siriya da Iraki da Libiya da Yemen da sauran kasashen da su dawo cikin hayacinsu su fahimci cewa an yi amfani dasu ne wajen kashe al'ummar wannan yankin da ruguzu kasashen yankin da kungiyoyin gwagwarmaya don biyan bukatun "Isra'ila" da Amurka". Sayyid ya ci gaba da kiran "Dukkanin wadanda har ya zuwa yanzu suke rike da makami daga dukkanin kungiyoyin 'yan ta'adda don kashe 'yan'uwansa da su fahimci cewa a halin yanzu lokaci ne da Amurka take shirin girbe kungiyar Da'esh, sannan kuma lamarin zai dawo kan sauran kungiyoyin". Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: Abin bakin cikin shi ne cewa akwai wani wanda yake tarwatsa kansa da kai harin kunar bakin wake don kashe dan'uwansa mutum. Don haka sai ya jaddada wajibcin kawo karshen wannan fitina da kuma yin dukkanin kokari wajen cimma hakan don kuwa idan har aka ci gaba da wannan ayyukan ta'addancin don cimma manufar Amurka, to babu makawa zai zame mana dole mu yake shi, wanda hakan yana kara tabbatar da ingancin matsayar da muka dauka na tafiya Siriya ne. Don haka sai Sayyid ya sake jaddada cewar za su ci gaba da kasantuwa a duk inda ya wajaba su kasance shin a garin Halab ne ko kuma wanin Halab din saboda Palastinu da al'ummar Palastinu.