Ya kara da cewa wannan cibiyar ta buga kur’anin ne tare da samun izinin daga cibiyar Azahar, takardar iznin tana dauke da lamba 25 a ranar 19/4/2011, alhali akwai manyan kura-kurai a cikin bugun wanda jami’ar Azahar ba ta yi la’akari da shi ba.
Malamin ya ce bai halasta a yi amfani da wannan kwafin kur’ani ba, kuma ya umarci dukkanin usulmin Palastine da su tatatra duk wani kwafi da ke a hannunsu su mika ga ofishin kula da harkokin shari’a, domin yin dubi kana bin da za a yin a gyara.