A hudubar sallar Juma'arsa a babban Masallacin Juma'ar birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a yau: Ayatullahi Ahmad Khatami ya tabo bakar siyasar Amurka da mahukuntan Saudiyya na kokarin sake farfado da kungiyar ta'addanci ta munafukai da suke adawa da tsarin Musulunci a kasar Iran tare da ware miliyoyin kudadena dalar Amurka;Yana mai fayyace cewa: Manufar wannan bakar siyasa ita ce yin amfani da kungiyar ta'addancin ta munafukai a kan al'ummar yankin gabas ta tsakiya ciki har da kasar Iran kuma mahukuntan Saudiyya sun dauki alhakin wadata kungiyar da kudade da makamai.
Ayataullahi Khatami ya jaddada cewa: A fili yake cewa kungiyar ta'addanci ta munafukai ta riga ta rushe kuma duk wani kokari damanyan kasashen duniya karkashin jagorancin Amurka da 'yan koranta na yankin gabas ta tsakiya zasu yi na sake farfado da kungiyar ba zai kai ga samun nasara ba.
Ayatullahi Khatami ya kuma tsakuro wani abu daga cikin ayyukan ta'addancin kungiyar munafukai ta Mujahidin Khaliq na kashe-kashen gilla da suka kai ga shahadan mutane kimanin dubu sha bakawai a sassa daban daban na kasar Iran.
Tun kafin wannan lokacin dai kasashen da suke kiyayya da kasar Iran a yankin gabas ta tsakiya su ne kan gaba wajen daykar nauyin kungiyar da kudadensu domin cutar da jamhuriyar muslunci, amma kuma makircinsu bai yi nasara ba.