Kamfanin dillancin labaran kur’ani na Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai da hulda da jama’a na cibiyar al’adun muslunci cewa, an gudanar da zaman taro mai taken mata a mahangar muslunci a birnin Abuja, wanda ofishin yada al’adu na Iran da ke Abuja ya dauki nauyin shiryawa.
An bude taron ne da karatun ayoyi na kur’ani mai tsarki daga bakin Sa’id Omidi, daga nan kuma aka shiga gabatar da jawabai kan matsayin mata da muhimmancin rawar rawar da suke takawa a cikin kowace al’umma.
Shugaban ofishin yada ala’adu na Iran a Abuja ya gabatar da jawabi dangane da matsayin mata a mahangar addinin muslunci, da kuma irin nauyin da ya rataya a kansua cikin rayuwar yau da kullum ta jama’a, da kuma ta iyali.
Shi ma a nasa bangaren shugaban reshen jami’ar Almustafa (SAW) da ke Kano ya gabatar da nasa jawabin, inda ya mayar da hankali kan matsayin mata a cikin ayoyin kur’ani da kuma hadisan ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka, kamar yadda shi ma Nuruddin Abdulmalik wani malami a jami’ar Ahmadu Bello Zaria ya gabatar da nasa jawabin kan wannan take.
Kamar ydda kam wasu daga cikin masana da suka halarci wurin duk sun gabtar da nasu kasidun wadanda suka tabo bangarori daban-daban da mata suke taka muhimmiyar rawa a cikin rayuwar zamantakewa ta kowace irin al’umma a duniya, ta yadda ya zama mata su ne babban gishikin tarbiya a cikin rayuwa ta yau da kullum ta iyali.
Daga karshe an bayar da wasu kyautka na musamman ga wadanda suka amda wasu tambayoyi da aka yi kan mata a mahangar addinin muslunci.