IQNA

Yaro Ya Hardace Kur’ani Cikin Watanni uku A Palastine

23:17 - August 22, 2016
Lambar Labari: 3480734
Bangaren kasa da kasa, wani karamin yaro mazunin yankin zirin Gaza ya hardace kur’ani mai tsarki cikin watanni uku.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na mubashir 24 cewa, Aiman Isma’il Astal yaro ne karami dan shekaru 12 da haihuwa kuma mazaunin yaniin Gaza wanda ya hardace kur’ani mai tsarki baki daya acikin watanni uku.

Aiman ya kasance yana hardar kur’ani a cikin mafi sa’oinsa na rana, kamar yadda kuma duk da haka yana mayar da hankali ga karantnsa na makaranta, inda shi ne dalibi na farko a jinsu.

Haka nan kuma ya kasance yana tsara lokutansa nma rana tun daga safe har zuwa yamma a kan dukaknin abubwan da yake yi, inda tun daga 9 na safe yak an zauna har zuwa zuhur domin karatu da hardar kur’ani idan ba a karatu a makaranta, idan kuma ranar karatu ce, yak an bari sai bayan ya dawo daga makaranta.

Isma’il Astal mahaifin Aiman malamin jami’a ne, kuma ya bayyana cewa ya horar da dansa a kan tafarkin addini da son kur’ani, kamar yadda shi ma mahaifansa suka koyar da shi, wanda hakan y aba yarinsa damar hardace kur’ani mai tsarki cikin watanni uku daga lokacin da ya fara harda.

Ya kara da cewa, tun yana yaro karami ya hardace kur’ani mai tsarki, wanda hakan ya sanya shi ma abin kauna a wajen mutane albarkacin littafi mai tsarki, wanda kuma ko shakka babu duk wata daukaka tana tattare ne a cikin yin aiki da abin da kur’ani ya umarce mu, kasantuwar cewa shi ne umarnin Allah gare mu.

  1. 3524658

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna
captcha