Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na nadorcity.com cewa, an gudanar da taron kammala horon ne a a makarantar Imam Malik da ke yankin Aulad Ibrahim a cikin lardin nazur.
Bayanin ya ce wannan horo ana gudanar da shi ne kawaia cikin lokacin bazara a lokacin da aka yi hutun makarantu.
Kimanin cibiyoyi9n kur’ani 155 nesuka shiga wannan horo, 124 daga cikinsu na maza ne, 31 kuma na mata, kamar yadda kuma mahaifan yaran sun halarci wurin da aka rika gudanar da horon.
Maimun Brisul it ace shugabar cibiyar kula da harkokin ilimi a lardin Nazur ta bayyana cewa, wannan bayar da horo yana da muhimamnci matuka ga dalibai, musamamn ma ganin cewa yana kara taimaka musu a wajen karatu da hardar kur’ani da sanin ka’idojinsu.
Muhimamn abubuwan da akakoyar dai sun hada da harda da kuma karatu na tartili, haka nan kuma an bayar da kyautuka ga wadanda suka nuna kwazo a wajen taro na bayar da horo.