Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum sabi cewa, an gudanar da taron mika wannan labule da aka dunka tun shekara ta 1830 ne tare da halartar wasu daga manyan jami’an gwamnatin masar, da kuma wasu daga cikin jam’ian diplomasiyya na wasu kasashen ketare.
Isma’il Sirajuddin shi ne shugaban dakin karatu na birnin Iskandariya ya bayyana cewa, hakika wannan lbule yana matsayin wani babban abin tarihi wanda aka dinka a kasar Turkiya, wanda misrawa suka yi aikinsa.
Yashar Hilmi shi ne wanda ya mallaki wannan labule, ya byyana cewa kasantuwar wannan labule a cikin dakin karatu na birnin Iskandariya, hakan yana da matukar tasiri a gare shi da kuma tarihin muslunci.
Fiye da shekaru 600 da suka gabata ne dai ake gudanar da wannan aiki na canja labulan dakin ka’abah, kuma ana dinka shi ne da zare wanda kasha 50 daga cikin na alhariri ne, yayin sauran zaren ake amfani da mai launin azurfa, wanda yake kawata dakin a duk lokacin aikin ibada da musulmi suke gudanarwa a kowace shekara.