Rahoton ya kara da cewa, minista mai kula da harkokin tsaro na cikin gida a kasar ta Canada Rolg Godal ya bayyana cewa, gwamnati ta amince a hukumance da wannan mataki, kuma hakan zai kara baiwa mata musulmi damar shiga aikin 'yan sanda a kasar ba tare da jin wata takura ba.
Yanzu haka an gabatar da nau'oin hijabi maikalar tufafin 'yan sanda na kasar Canada, wanda 'yan sanda mata musulmi za su rika amfani da shi a lokutan aiki.
Tun daga lokacin da aka kafa rundunar 'yan sanda a kasar ta Canada a cikin shekara ta 1800, wannan shi ne karon farko da aka amince a hukumance da saka hijabi ga 'yan sanda mata a kasar.