Kamfanin dillanicn labaram kur’ani na iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na al-alam cewa, rahotanni daga kasar Bahrain din sun bayyana cewar jami'an tsaron kasar wadanda suka yi wa garin kawanya sun hana masallata gudanar da sallar Juma'a a masallacin Imam Sadiq (a.s) da ke garin, wanda hakan shi ne karo na shida kenan da suke hana gudanar da sallar Juma'ar a wannan masallacin wanda Ayatollah Sheikh Isa Qasim din yake jagoranta.
A makon da ya wuce ma dai malamai daban-daban a kasar sun yi Allah wadai da kuma kakkausar suka ga mahukutan kasar Bahrain din wadanda suke samun goyon bayan gwamnatin Saudiyya sakamakon hana masallata sauke farali a wannan masallaci wanda ake kirga shi a matsayin mafi girman taron sallar Juma'a a duk fadin kasar. Malaman dai sun kirayi al'ummar kasar da su gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai da wannan mataki da gwamnatin ta dauka.
Tun dai bayan da gwamnatin Bahrain din ta sanar da kwace takardar dan kasa na Sheikh Isa Qasim, jami'an tsaron suke ci gaba da takurawa al'ummar kasar Bahrain din musamman ma na garin na Al-Diraz wadanda suka taru a gidan shehin malamin da nufin ba shi kariya daga cutarwar jami'an tsaron gidan sarautar Al Khalifa da suke mulkin kama karya a kasar.