Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Dakar.icro cewa, wannan nashara an buga ta ne a cikin shafuka 4, kuma an samar da kwafi 300 a mataki na farko, domin yada fahimtar kur’ani da hadin kan musulmi.
Shi dai wannan taron karawa juna sani shi ne irinsa na farko da aka gudanar a yammacin nahiyar Afirka, wanda karamin ofishin jakadancin kasar Iran da ke birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal ya dauki nauyin shiryawa da gudanarwa, tare da halartar manyan jami’an gwamnati da kuma malamai gami da jami’an diplomasiyya.
Dakar ta daukin nauyin wani taron makamancin wannana cikin shekarar da ta gabata, wanda ke da taken annabi Ibrahim (AS) zuwa ga manzon karshe Muhammad (SAW) amma tanadin da aka yi wa tarina wannan karon ya dara na kowane lokaci.