IQNA

Jam'iyyar Masu Ra'ayin 'Yan Mazan Jiya Za Ta Rufe Masallatai A Holland

23:55 - August 27, 2016
Lambar Labari: 3480750
Bangaren kasa da kasa, Jam'iyyar masu ra'ayin 'yan mazan jiya a kasar Holland ta sha alwashin rufe masallatai da makarantun addinin musulunci a kasar matukar dai ta lashe zabe mai zuwa.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, Shafin yanar gizo na tashar Alhurrah ya bayar da rahoton cewa, jam'iyyar conservative ta kasar Holland ya sanar da cewa, daya daga cikin muhimman abubuwan da za ta fara aiwatarwa idan ta lashe zaben majalisar dokokin kasar shine rufe masallatai da kuma cibiyoyin musulmi gami da makarantun da ake koyar da addinin muslunci.

Sakamakon wani jin ra'ayin jama'a da aka gudanar da a kasar ta Holland ya yi nuni da cewa, jam'iyyar ta Conservative tana kan agaba, lamarin da ke nuni da dcewa akwai yiwuwar ta sau nasara a zaben wanda zaa gudanar a cikin watan Maris na shekara mai kamawa.

Geert Wilders dan majalisar dokokin kasar Holland mai tsananin kiyya da addinin muslunci ya mamba a ne a wannan jam'iyya.

Wannan jam’iyya ta sanar da cewa tana shirin daukar matakan da take ganin sun dace a kan muuslmi idan har ta ci zabe, inda za ta hara,ta ayyukan muuslmi a kasar baki daya.

3525491

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna
captcha