IQNA

An Rufe Asusun Ajiya Na Wasu Musulmi A Wasu Bankunan Amurka

23:52 - August 28, 2016
Lambar Labari: 3480753
Bangaren kasa da kasa, Babbar cibiyar musulmin kasar Amurka ta sanar da cewa, wasu daga cikin bankunan kasar Amurka sun rufe a susun ajiya na wasu daga cikin musulmin kasar da ske yin ajiya a wadannan bankuna.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin cibiyar Daily Caller, inda ta sanar da cewa musulmin da wannan lamari ya shafa sun koka matuka dangane da yadda ake nuna musu wariya da banbanci saboda addininsu, duk kuwa da cewa sun 'yan kasa ne kamar kowane dan kasa.

Bayanin ya ce har yanzu babu wani bayani da ya fito daga bangaren gwamnatin Amurka ko kuma bankunan da suka dauki wannan mataki kan musulmi, a kan cibiyar ta ce za ta bi kadun wannan batu a shar'ance, domin hakan ya yi hannun riga da dukkanin dokoki na kasar Amurka.

Daga cikin bankunan da suka rufe asusun ajiya na wasu muslmin kasar ta Amurka akwai American bank, Ches Bank, wealth Fargo Bank, wadanda dukkaninsu sun tabbatar wa cibiyar cewa musulmin da aka nrufe wa asusun ajiya ba su karya ko daya daga cikin dokoki da ka'idoji na ajiya abanki ba.

Musulmi a kasar Amurka dai suna fuskantar matsaloli da suka hada da tsangwama a wasu jahohi da kuma nuna musu banbanci.

3525582

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna
captcha