Bayanin yace 'yan ta'addan sun tsere daga yankin bayan arangama mai tsanani tsakaninsu da dakarun Syria da kawayensu, inda a jiya 'yan ta'addan suka gudu suka bar tarin makamai da suka hada da rokoki da makamai masu linzami da tankokin yaki, gami da sanadarai na harhada bama-bamai.
Kungiyoyin 'yan ta'adda da dama ne suka tare a yankin na Daraya tun fiye da shekara guda da ta gabata, wanda kuma a nan hubbaren Sayyida Sukaina (S) jikar manzon Allah yake, inda suka ragargaza ginin hubbaren nata da sauran wurare na tarihi da ke yankin.
Yanzu haka jami'an sojin na kasar Syria sun shiga aikin share tituna daga abubuwan da 'yan ta'addan suka bari, domin tabbatar da cewa an kawar da nakiyoyin da suka dasa, kafin barin al'ummar yankin da suka yi hijira su koma gidajensu.