IQNA

Markel Ta Yi Kakkausar Suka Kan Rufe Kofofin Shiga Turai Ga 'yan Gudun Hijira

23:21 - August 29, 2016
Lambar Labari: 3480757
Bangaren kasa da kasa, Shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Markel ta yi kakkausar suka dangane da hana musulmi 'yan gudun hijira shiga cikin kasar nahiyar turai.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga Shafin yada labarai na First Post ya habarta cewa, shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Markel ta bayyana matakin da wasu daga cikin kasashen turai suke dauka kan musulmi 'yan gudun hijira da cewa ya yi hannun riga da 'yan adamtaka.

Markel ta ce tana fatan kasashen kungiyar tarayyar turai da suka daukin matakin hana 'yan gudun hijira musulmi shiga kasashen za su sake yin nazari kan wannan mataki, domin kuwa hakan ya sabawa manufofin kafa kungiyar.

Tun bayan da 'yan gudun hijira na kasashen larabawa musamman an na Syria suka fara shiga nahiyar turai, wasu daga cikin kasashen suka sanar da rufe iyakokinsu, musamman ga musulmi daga cikinsu.

3526183

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna
captcha