IQNA

Gwamnatin Kasar India Za Ta Hukunta Zakir Nike

23:23 - August 29, 2016
Lambar Labari: 3480758
Bangaren kasa da kasa, Ma'aikatar harkokin cikin gida a kasar India ta sanar da cewa za ta hukunta Zakir Nike bisa zargin cewa yana yada akidar tsatsauran ra'ayi a tsakanin musulmin kasar India.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto Jaridar Ummat ta kasar Pakistan ta bayar da rahoton cewa, ma'aikatar harkokin cikin gida a kasar India ta bukaci kotun hukunta ayyukan ta'addanci a kasar da ta dauki matakan dakatar da ayyukan dukkanin cibiyoyi da ke karkashin Zakir Nike, sakamakon yada tsatsauran ra'ayi a kasar.

Bayanin ya ce wannan mataki zai hada da rufe tashoshinsa na talabijin, da kuma makarantu, haka nan kuma za a gabatar da tuhuma a kansa kan saka matasa a cikin kungiyoyi na 'yan ta'adda, domin kuwa a cewar ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta India, dukkanin matasan kasar ad suka shiga cikin kungiyoyin 'yan ta'adda da ke yaki a Syria da Iraki almajiransa ne.

A nata bangaren gwamnatin kasar Bangaladash ta ce wadanda suka kai hare-haren ta'addanci a kasar a kwanakin baya suna daga cikin mabiyansa, wanda hakan ne yasa aka haramta masa shiga kasar.

3526161

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna
captcha