Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, jami’an tsaron gwamnatin Saudiyyah sun kame sheikh Fahmi Zainuddin daga yankin Saihat da Sayyid Jafa Alawi daga yankin Safawi dukkaninsu daga lardin Qatif da ke gabashin saudiyya.
Kwamitin kare hakkin bil adama na Saudiyya ya ce babu wani bayani har yazu dangane da dalilan kama su.
Kwamitin ya kara da cewa Sheikh fahami Zaunuddin da kuma Sayyid Jafar Alawi, suna daga cikin malamai masu gudanar da harkoki na addini a yankunan da e cikin lardin Qatif.
Kafin wannan lokacin ma jami’an tsaro na Saudiyya sun kame wani dan kasar a yankin Ihasa.
Wannan mutum mai sun aAli Khalifa, jami’an tsaron Saudiyya a cikin kayan saki sn kai farmai ne kan ofishinsa a inda yake aiki, inda suka kame suka yi awon gaba da shi.
Shi ma dai har yanzu babu wani bayani kan dalilan kama shi da jami’an tsaron suka bayar.