Ta ce tun bayan da aka kame su ake tsare da su kuma suna butakar kulawa ta fuskar lafiya musamman shi malam, amma kuma wadanda suka tsare shi ba su mayar da hankali kan hakan ba.
Dangane da abin da kira jita-jita da ake yadawa kan abubuwan da ake cwa ya fada, ta ce babu wani wanda ya gana da shi inda ban da ‘ya’yansa da kuma wasu daga cikin danginsa na jinni, a kan hakan duk wani abu da aka ji daga wani wanda ba su ba, to ya kamata a tabbatar da kafin daukar duk wani mataki.
Tun a karshen shekarar da ta gabata ce dai jami’an tsaro na soji a Najeriya suka kadama da hari kan gidan shekh Ibrahim Zakzaky a gain Zaria, inda suka kasha daruruwan fararen hula da suka hada da mata da kananan yara, da kuma kam wasu masu tarin yawa da aka jikkata da dama daga cikinsu.
Wannan mataki dai ya zo bisa hujjar cewa wasu daga cikin mabiyansa sun tare wa babban hafsan hafsoshin sojin kasa hanya a lokacin da yake wucewa.