IQNA

Jerin Gwanon Kin Jinin La’antacciyar Itaciya A Bahrain

15:02 - September 11, 2016
Lambar Labari: 3480774
Bangaren kasa da kasa, dubban muuslmi a kasar Bahrain sun gudanar da jerin gwanon kin jinin la’antacciyar itaciya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ManamaPost cewa, tun daga shekaran jiya zuwa jiya an gudanar da jerin gwanon kin jinin la’antacciyar itaciya ta al Saud a kasar Bahrain baki daya.

Bayanin y ace daga cikin muhimman wuraren da aka gudanar da wannan jerin har da yankunan diraz da sauran yanunan da ke cikin gundumar Manama da kuma wasu yankunan na kasar.

Babbar manufar gudanar da wannan gangami dai ta ce nuna rashin amincewa da yadda masarautar iyalan gidan Saud ta wahabiyawa ta mamaye wurare masu tsarki na Makka da Madina tare da kafa ikonsu da siyasars a kan wadannan wurare mallakin dukkanin al’ummar musulmi na duniya baki daya.

Masu jerin gwanon sun yi kira da kubutar da wadannan wurare daga mamayar wahabyawa da ke samun goyon bayan yahudawa tare da aiwatar da manufofins kan al’ummar musulmi ta hanyar fakewa da makka da madina da wurare masu tsarki.

Kamar yadda kuma suka tir da Allawadai da shigar shugula da masarautar wahabiyawan Al Saud key i a cikin harkokin kasarsu, inda suka kafa masarautar iyalan gidan khalifah da ke tsananin kiyayya da mafi yawan al’ummar kasar wadanda mabiya mazhabar shi’a ne.

Daga karshe kuma suka nuna goyon bayansu ga dukaknin al’ummomin da masarautar wahabiyawan Al Saud ke zalunta acikinkasashen larabawa da na musulmi, tare da nuna alhini ga iyalan wadanda ta’addaninsu ya shafa.

3529414


captcha