IQNA

Jaridar Ra’ayul Yaum:

Mai Yiwuwa Mai Bada Fatawa Na Al Saud Ya Safka

19:53 - September 13, 2016
Lambar Labari: 3480777
Bangaren kasa da kasa, mai yiwuwa mai bayar da fatawa ga masarautar ‘ya’yan gidan Saud ya safka daga kan matsayinsa.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tasha al-alam cewa, Abdulrahman Sudais mai yin huduba a haram shi ne ya karanta jawabin Arafa maimakon babban mai bayar da fatawa na masarautar iyalan gidan Saud.

A kwanakin baya ne dai mai fatawar na masarautar yayan Saud Abdulaziz Al sheikh ya bayyana al’ummar musulmi na kasar Iran a matsayin kafurai, bisa hujjar da bayyana da cewa su jikokin masu bautar wuta ne.

Wannan furuci nasa dai tun daga lokacin har zuwa yanzu yana ci gaba da fuskantar suka daga musulmi a koina acikin fadin duniya da hakan ya hada har daga malaman wahabiya a cikin kasar ta Saudiyyah.

Ba a dai bayyana takaimai dalilin da yasa mai fatawar yaki yin huduba a wannan karo ba, bayan ya kwashe tsawon shekaru fiye da 35 yana gabatar da jawabin ranar Arafa sai a wannan karon ne bai gabatar ba, lamarin da ke nuni da cewa akwai wani takun saka a tsakaninsu.

Shi ma a nasa bangaren wanda ya gabatar da hudubar ya bayyana godiyarsaga bababn mai bayar da fatawar tae da bayyana sia matsayin mutumin da ya jima yana hidima ga abin da ya kira sunna, sai da bai yi Karin haske kan dalilan da suka hana shi ya gudanar da hdubara bana ba, kamar yadda bai gaya ma jama’a yadda aka yi ya zama shi ne mai hudubar ba.

Sai dai ya yi kokari domin ganin ya rage kaifin sukar da babban ma bayar da fatawar ke sha da kuma masarauta da yake wakilta, kan batun kafirta al’umma musulmi na kasar Iran da ya yi.

3529761


captcha