IQNA

An Bukaci Mayar Da Ranar Ghadir Hutu Na Kasa A Iraki

14:48 - September 19, 2016
Lambar Labari: 3480795
Bangaen kasa da kasa, fiye da ‘yan majalisar dokokin Iraki 100 sun bukaci a mayar da ranar Ghadir ta zama hutu na kasa baki daya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sautul Iraq cewa, Muhammad Likash daya daga cikin yan majalisar dokokin Iraki daga gungun Muwatin ya bayyana cewa, fiye da ‘yan majalisar dokokin Iraki 100 sun bukaci a mayar da ranar Ghadir ta zama hutu na kasa baki daya kamar sauran ranakun hutu.

Muhammad Likash ya ce idan aka yi la’akari da ranaun hutu na kasar dukkanin kasar ne baki daya, amma ranar Ghadir wasu lardunan hutu ne a hukumance wasu kuma bah utu ba ne, a kan hakan suna bukatar ya zama hutu na kasa baki daya, saboda mafi yawan al’ummar kasar suna gudanar da bukukuwa a ranar.

Kasar Iraki dai nan hubbaren shugaban muminai yake, wanda kuma a kasar ne mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah na kasar da kuma kasashen duniya daban-daban ke taruwa domin tunawa da wannan rana mai daraja.

Yanzu haka dai wannan takarda da fiye da ‘yan majalisa 100 suka rattaba wa hannu ta isa ga shugaban majalisar dokokin kasar ta Iraki domin yin dubi a kanta, wanda za a sana da bayani daga bisani.

3531145


captcha