IQNA

Sayyid Nasrullah A Lokacin Ganawa Da Maddahin

Shi’acin Ingila Ya Fi Wahabiyanci Da Sahyuniyanci Hatsari

11:00 - September 28, 2016
Lambar Labari: 3480814
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar Hizbullah a lokacin da yake ganawa da masu bege a hubbarori masu tsarki ya bayyana shi’acin Ingila a matsayin lamari mafi hadari a kan wahabiyanci da sahtuniyanci.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar alalam cewa, Sayyid Nasrullah ya bayyana abin da yake faruwa na yada wata mummunar akida da sunan bin mazhabar shi’a daga Ingila da cewa shi ne mafi hadari a kan akidar wahabiyanci da kuma yahudancin sahyuniya.

Ya bayyana wadannan mutane da suke watsa irin tunaninsu da sunan bin tafarkin iyalan gidan manzo da cewa, suna kokarin dutse hasken iyalan gidan manzo da kuma kawo fitina mafi muni a tsakanin al’ummar musulmi.

A kan haka ya ja hankalin masu bin tashoshi da shafukan yanar gizo da su yi hattara su banbance tsakanin mazhabar iyalan gidan manzo ta hakika da kuma ta turawa wadda aka kirkira domin domin dushe duk wani tasiri na hakikanin koyarwar manzo da iyalan gidansa tsarkaka.

Daga cikin abubuwan da wadannan mutane suke yi har da zagin wasu fitattun mutane daga cikin mutanen da yan sunna suke girmamawa, kamar yadda kuma suke cin zarafin wasu daga cikin matan manzo, wanda hakan ya yi hannun riga da koyarwar mazhabar shi’a.

Haka nan kuma dagane da abin da suke yi wanda shi ne hakikanin abin da yahudawa suka shirya domin rusa addini, shi ne kuma abin da suka shirya na kirkirar akidar wahabiyanci, to amma wannan yafi hadari domin kuwa shi da sunan mazhabar iyalan gidan manzo aka kirkire shi, yayin da kuma wahabiyanci dama akida ce da ke nisanta kanta da koyarwa iyalan gidan manzo, wadda ita koyarwar da manzo ya yi umarni da ayi riko da ita a bayansa tare da kur’ani mai tsarki.

Dangane da abin da yake faruwa a fagen siyasa a kasarsa kuwa, ya bayyana cewa dukkanin abin da yake faruwa Magana ce ta siyasa da bata da wata alaka da akida ko addinim domin kuwa Magana ce kare manufa da mahangar siyasa da kowane bangare yake da ita, wanda shi ne ya jawo dukkanin matsaloli na siyasa a kasar bai daya.

3533470


captcha