Kamfanin dillancin labaran kur’ani
na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar
alalam cewa, babban mai bayar da fatawa na masarautar wahabiyawa ta al saud
Abdulaziz alsheikh ya bayyana taron maulidin manzon Allah (SAW) da cewa aiki ne
na shirka.
Mutumin ya yi kira ga matasa wahabiyawa musamman da su yi hattara da shiga cikin duk wani abu mai alaka da maulidi domin kuwa a cewarsa ba shi da wani tushe a cikin musulunci bidi’a ce da aka kirkira wanda kuma yin hakan kafirci ne da shirka.
Amma dangane da tarukan zagayowar ranar da turawa suka kafa masarautar alsaud, Alsheikh ya bayyana wannan rana da cewa ran ace ta kasa baki daya, kuma dole ne a raya ta da taruka na tunawa da kafa wannan masarauta.
Ya ci gaba da cewa wannan ran ace da ya zama wajibi a kan dukkanin yan kasa da su taru su yi godiya ga Allah kan wannan babban alkhairi da ya yi musu na samun kafa masarautar iyalan gidan Saud.