IQNA

Keta Alfarmar Masallaci Da Masu Salla A Birnin Landan

23:34 - October 05, 2016
Lambar Labari: 3480827
Bangaren kasa da kasa, wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun jefa naman alade a kan masallacin Rahman da ke yankin Samars town a cikin birnin Landan na kasar Birytaniya.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na camdennewjournal cewa wasu mutane ne biyu da suke sanye da kayan yansanda suka jefa naman alade a kan masallacin Rahman da ke yankin Samars town a cikin birnin Landan na kasar Birytaniya kuma suka dauki hoton abin da suka aikata.

Hilal Ahmad daya ne daga cikin mambobin kwamitin masallacin ya bayyana cewa, ya ga mutanen biyu a lokacin da suke jefa naman alade kan masallacin a lokacin da ake salla, da farko ya yi zaton cewa ‘yan sanda ne, amma sai ya gas hi ma suna jefa masa naman alade, a lokacin sai ya fahim ci cewa masu tsokana ne.

Ya kara da cewa wannan dai shi ne karon farko da wani abu mai kama da haka a farua cikin shekaru takwas a jere da ya kwashe yana zuwa wannan masallaci yana gudanar da ibada.

Bayan yan mintuna da faruwar hakan, jami’an ‘yan sanda sun isa wurin tare da daukar matakan tsaro domin tabbatar da cewa sun bayar da kariya ga musulmi da suke salla a cikin masallacin.

Addinin mulsunci dai yana a matsayin addini na biyu mafi girma a kasar Birtaniya, inda yanzu haka akwai masallatai kimanin 600 da makarantun addnin muslunci guda 60 da aka gina a kasar.

3535799


captcha