IQNA

Keta Alfarmar Masallaci A Kasar Jamus

21:41 - October 06, 2016
Lambar Labari: 3480830
Bangaren kasa da kasa, wasu masu tsananin adawa da musulunci a kasar Jamus sun kai farmaki kan wani masallaci a garin Ham na kasar.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yana gizo na Anatoli cewa, wani gungu na masu tsananin adawa da musulunci a Jamus sun kai farmaki kan wani masallaci a garin Ham tare da keta alfarmarsa.

Wadannan mutane wadanada masu tsatsauran ra’ayi ne na kin muslunci da kiuma bakia kasar ta jamus, sun ta rubuce-rubuce kan bangayen masallacin na nuna kyama ga addinin muslunci, da kuma zanen sakandami.

Daga abin da suke rubutawa har da cewa addinin mslunci shi ne tushen duk wani ta’addanci, saboda haka muslunci addinin ta’addanci ne, dole ne muuslmi su bar kasar jamus su koma kasashen, ‘yan Nazy kuma su wansu.

Thomas Peter man shi ne magajin garin birnin na Ham ya yi alawadai da kakakusar murya, tare da jadda cewa ba zu taba amincewa da irin wannan lamari ban a takura ma wasu saboda akidarsu ko addininsu, alhali ba su tsarewa kowa komai ba a kasar.

Haka nan kuam ya jaddada cewa za a dauki matakan da suka dace wajen kame dukkanin wadanda suke da hannua cikin lamarin domin gurfanar da su a gaban kuliya.

Masu dauke da irin wannan mummunar akidar a kasar Jamus dai sanannanu ne, kuma bayau suka fara ba, sai sakamakon ayyukan ta’addanci da wahabiyawa suke aikatawa da sunan addinin musulunci a duniya a halin yanzu.

3536034


captcha