IQNA

Kudirin UNESCO Ksan Masallacin Aqsa Na Tattare Da Hikima Kuma Na Tarihi Ne

20:37 - October 17, 2016
Lambar Labari: 3480860
Bnagaren kasa da kasa, malaman musulmi da kuma masana a birnin quds sun nuna farin cikinsu matuka dangane da daftarin kudirin UNESCO kan masallacin aqsa.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran palastinu cewa, n addini da kuma masana a birnin quds sun nuna gamsuwa da matakin da hukumar kula da harkokin ilimi da traihi ta majaliasar dinkin duniya ta dauka na kare martabar masallacin aqsa.

Kungiyar UNESCO dai ta gabatar da wani daftarin kudiri nea zaman da mambobinta suka gudanar, inda ta bayyana masallacin aqsa da yahudawa ke bugun gaba da cewa na su, kngiyar ta ce wannan masallaci mallakin musulmi ne.

Bayanin ya kara da cewa dukkanin ayyukan da yahudawan sahyuniya suke aikatawa kan wannan wuri ya sabawa kaida, da hakan ya hada da killace wurin da hana musulmi shiga domin gudanar da ayyukan ibadarsu.

Kamar yadda kuma kungiyar ta UNESCO ta yi kkkausar da Allawadai da kafa bango da yake dauke da wutar lantarki, domin hana palastinawa yan asalin wurin isa sauran yankunansu.

Wannan daftarin kudiri dai wasu daga cikin kasashen larabawa da suke amatsayin mambo a hukumar ne suka gabtr da shi, kuma aka gudanar da zaman kada kuri’a a kansa tare da halartar wakilan dukkanin mambobi.

Kasashe 24 ne suka kada kri’ar amincewa da shi, yayin da 6 suka amincewa da hakan, sauran kasashe 26 kuma bas u bayyana ra’ayinsu na amincewa ko kin amincewa ba, yayin kasashe biyu kuma bas u uffan ba.

Bbbar manufar wannan daftarin kudiri dai it ace tabbatar ma duniya da cewa haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta hurumin keta alfarmar wurare masu tsarki na musulmi da kiristoci, tare da tabbatar da cewa wannan wuri na musulmi ban a yahudawa ba.

3538315


captcha