IQNA

Ministan Al’adun Masar:

Kudirin UNESCO Babban Kayi Ne Ga Amurka Da Isra’ila

22:41 - October 19, 2016
Lambar Labari: 3480864
Bangaren kasa da kasa, Hilmi Al-namnam ministan al’adu na Masar ya bayyana kudirin UNESCO da ke tabbatar da malalkar masallacin aqsa ga musulmi da cewa kayi ne ga Amurka da Isra’ila.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin tanar gizo na alwafd cewa, Hilmi Al-namnam ministan al’adu na Masar ya bayyana kudirin UNESCO da ke tabbatar da malalkar masallacin aqsa ga musulmi da cewa kayi ne ga Amurka da Isra’ila da ma dukkanin gwamnatocin da ke goyon bayan siyasarsu.

Ya ci gaba da cewa ko shakka babu wannan babbar nasara ce ga dukkanin msuulmi da larabawa da kuma palastinawa, domin kuwa an jima ana yin ruwa kasa na shanyewa, sai a wannan karon ne gaskiya ta yi halinta.

A jiya ma hukumar ta UNESCO ta sake bijiro da wannan daftarin kudirin kudiri a birnin Paris, inda aka sake kada kuri’a a kansa, kuma kasashen da suka amince da shi suna nan kan bakansu yayin da yan tsirarun da suka ki amincewa da shi su ma suka tsaya kan bakansu.

Kasashe 24 ne suka nuna gamsuwarsu da amincewarsu da wannan daftarin kudiri, yayin da kuma wasu 6 mafi yawansu na turai suka ki amincewa da shi.

Abin tuni a nan dai shi ne a cikin wannan daftarin kudiria aka gabtar a cikin makon da ya gabata, ya bayyana masallacin aqsa a matsayin mallakin musulmi ba yahudawa ba, sabanin abin da Isra’ila take rayawa na cewa masallacin na yahudawa ne, haka nan kuma kudirin yayi Allawadai da cin zarafin musulmi da Isra’ila take yi, da kuma keta alfarmar wurare masu tsarki na musulmi da kuma kiristoci.

3539156


captcha