IQNA

Limamin Juma’a A Tehran:

Hadewar Al’ummomi Ne Karshen Masu Girman Kai / Darussa Daga Sadukantarwar Imam Hussain (AS)

23:49 - October 21, 2016
Lambar Labari: 3480870
Bangaren kasa da kasa, wanda ya jagoranci sallar juma’a Tehran ya bayyana abin da yake faruwa na fadar al’ummomin duniya dangane da zaluncin masu girman kai a matsayin babban ci gaba.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, Hojjatol Islam Kazem Siddighi wanda ya jagorancin sallar Juma’a a Tehran, yay i bayani kan irin tsayin daka da Imam Hussain (AS) yay i wajen kare gaskiya da kuma sadaukantarwar da ya yi da rayuwarsa domin hakan.

Ya ce Imam Hussain (AS) ya koyar da dukkanin yan adam imani da gaskiya da kuam tsayawa a kanta koda za a rasa komai na duniya, wanda kuma wasu yin yi koyi da hakan da suka hada da musulmi da ma wadanda ba musulmi, saboda abin da suka gani na koyi daga abin da Imam Hussain (AS) ya koyar na yaki da zalunci da riko da gaskiya da adlaci.

Limamin Juma'ar Tehran ya yi tir da shirun da kasashen duniya su ka yi akan laifukan yakin da Saudiyya ta ke yi a Yamen.

Hujjatul-Islam Wal-Muslimin Kazim Sadiqy, ya yi ishara a cikin hudubarsa ta juma'a da laifukan yakin da Saudiyya ta ke tafkawa a kasar Yamen,musamman kashe kananan yara da kuma harin bayan nan da ta kai a wurin ta'aziyya.

Limamin na Tehran ya kwatanta kisan da Saudiyyar ta ke yi wa kananan yara a Yamen da irin wanda Haramtacciyar Kasar Isra'ila ta ke yi wa Palasdinawa.

Har ila yau, limamin Tehran din ya ambaci atisayenda sojojin saman Iran su ka yi a karo na 6, sannan ya ce; Sako ne na kawance ga al'ummun wannan yankin, a lokaci daya kuma gargadi ne ga masu adawa da Iran.

Malamin ya ci gaba dajan hankulan al’ummar musulmi da su zama cikin fadaka kan yadda ake jan akalarsu ba tare da sun ankara ba, domin kuwa ana hankoron cinikar da su ga yahudawan sahyuniya da sunan addini.

Kamar yadda kuma yay i ishar ada yadda masarautar iylan Saud take daukar nauyin yada akidar wahabiyanci da haifar da rikici da fitina a tsakanin al’ummar msuulmi, ta yadda hakan zai shagaltar da su, yayin da makiya kuma suke amfani da hakan wajen ci gaba da yi wa musulmi illa a dukkanin bangarori.

Daga karshe ya jaddada wajabcin yin tsayin daka domin fuskantar makiya da kuma munafukai daga cikin gwamnatocin musulmi da suke rusa kasashen larabawa da na musulmi saboda banbanci mahanga ta siyasa, domin kuma su dadama yahudawa da uwayen gidancu.

Kasar Saudiyya ce dai kan gaba wajen mara baya ga kungiyoyin yan ta’adda a duniya da suke kai hare-hare da sunan jihadi, inda suke kashe musulmi da ma wand aba musulmi, bisa akidarsu ta ganin kowa kafuri ne matukar dai bai yi imani da akidar wahabiyanci ba.

3539499


captcha