Mutumin dan shekaru 53 dan kasar Masar ne da yafito daga garin Faisal a cikin gundumar Jizah, kuma yana da nufin sayar da wannan kwafin kur’ani ne mallakin hukumar kula da ayyukan yawon bude ido ta kasar, a kan kudi dalar Amurka miliyan guda da dubu 200.
Jami’an ‘yan sanda sun kasance suna bibiyar wannan mutum, inda suka rutsa da shi a cikin gidansa, kuma suka samu wannan kwafin kur’ani ajiye a cikin gidansa, a tar kayan tarihi mallakin kan haka an kama shi da laifin satar kayan tarihi mallakin gwamnatin kasar.